Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 11:43-54 Littafi Mai Tsarki (HAU)

43. Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna son mafifitan mazaunai a majami'u, da kuma gaisuwa a kasuwa.

44. Kaitonku! Kuna kama da kaburburan da ba a gani, waɗanda mutane suke takawa da rashin sani.”

45. Sai wani a cikin masanan Attaura ya amsa masa ya ce, “Malam, faɗar haka fa, mu ma, ai, ka ci mutuncinmu.”

46. Sai Yesu ya ce, “Ku kuma kaitonku, masanan Attaura! Don kuna jibga wa mutane kaya masu wuyar ɗauka, ku da kanku ko ɗan yatsa ba kwa sawa ku tallafa musu!

47. Kaitonku! Don kuna gina gubbobin annabawan da kakanninku suka kashe.

48. Wato, ku shaidu ne a kan kun yarda da ayyukan kakanninku, ga shi, su ne fa suka kashe su, ku kuwa wai har kuka gina musu gubbobin!

49. Shi ya sa hikimar Allah ta ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni, su kashe waɗansu,’

50. don alhakin jinin dukan annabawa da aka zubar tun daga farkon duniya, a bi shi a kan mutanen wannan zamani,

51. wato, tun daga jinin Habila, har ya zuwa na Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagaden hadaya da Wuri Mai Tsarki. Hakika, ina gaya muku, duk za a bi shi kan mutanen wannan zamani.

52. Kaitonku, masanan Attaura! Don kun ɗauke mabuɗin ilimi, ku kanku ba ku shiga ba, kun kuma hana masu son shiga su shiga.”

53. Da ya fito daga wurin, sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara matsa masa ƙwarai, suna tsokanarsa ya yi maganar abubuwa da yawa,

54. suna haƙwansa su burma shi a cikin maganarsa.

Karanta cikakken babi Luk 11