Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 11:16-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Waɗansu kuwa, don su gwada shi, suka nema ya nuna musu wata alama daga Sama.

17. Shi kuwa da ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu a kan gāba, zai lalace. Haka kuma, in gida ya rabu a kan gāba, zai baje.

18. In kuma Shaiɗan ya rabu a kan gāba, yaya mulkinsa zai ɗore? Ga shi, kun ce da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu.

19. In kuwa da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu, to, 'ya'yanku fa, da ikon wa suke fitarwa? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku.

20. Ni kuwa in da ikon Allah nake fitar da aljannu, ashe, Mulkin Allah ya zo muku ke nan.

21. In ƙaƙƙarfan mutum ya yi ɗamara sosai, yana tsaron gidansa, kayan gidansa lafiya suke.

22. In kuwa wanda ya fi shi ƙarfi ya fāɗa masa, ya kuma rinjaye shi, sai ya ƙwace duk makaman da ya dogara da su, ya kuma rarraba kayansa ganima,

23. Wanda ba nawa ba ne, gāba yake yi da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.”

24. “Baƙin aljan, in ya rabu da mutum, sai ya bi ta wurare marasa ruwa, yana neman hutawa. In ya rasa, sai ya ce, ‘Zan koma gidana da na fito.’

25. Sa'ad da kuwa ya komo gidan ya tarar da shi shararre, ƙawatacce,

26. Daga nan sai ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum kuwa ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa.”

27. Yana faɗar haka, sai wata mace a taron ta ɗaga murya ta ce masa, “Albarka tā tabbata ga wadda ta haife ka, wadda ka sha mamanta.”

Karanta cikakken babi Luk 11