Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 1:53-65 Littafi Mai Tsarki (HAU)

53. Mayunwata ya ƙosar da abubuwan alheri,Mawadata kuwa ya sallame su hannu wofi.

54. Ya taimaka wa baransa Isra'ila,Domin yana tunawa da jinƙansa.

55. Ya cika faɗarsa ga kakanninmu,Ga Ibrahim da zuriyarsa, har abada.”

56. Maryamu kuma ta zauna tare da Alisabatu wajen wata uku, sa'an nan ta koma gida.

57. To, lokacin Alisabatu na haihuwa ya yi, ta kuwa haifi ɗa namiji.

58. Sai maƙwabta da 'yan'uwanta suka ji yadda Ubangiji ya ji ƙanta ƙwarai, har suka taya ta farin ciki.

59. Sai ya zamana a rana ta takwas suka zo yi wa ɗan yaron kaciya. A dā za su sa masa sunan ubansa, Zakariya,

60. amma uwa tasa ta ce, “A'a, Yahaya za a sa masa.”

61. Sai suka ce mata, “Ai kuwa, ba wani ɗan'uwanku mai suna haka.”

62. Sai suka alamta wa ubansa, suna neman sunan da yake so a sa masa.

63. Sai ya nema a ba shi allo, sa'an nan ya rubuta, “Sunansa Yahaya.” Duka suka yi mamaki.

64. Nan da nan ya sami baki, kwaɗon harshensa ya saku, ya fara magana, yana yabon Allah.

65. Sai tsoro ya kama dukan maƙwabtansu. Aka yi ta baza labarin duk waɗannan al'amura ko'ina a dukan ƙasa mai duwatsu ta Yahudiya.

Karanta cikakken babi Luk 1