Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 1:35-51 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Mala'ikan ya amsa mata ya ce,“Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki,Ikon Maɗaukaki kuma zai lulluɓe ki.Saboda haka Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.

36. Ga shi kuma, 'yar'uwarki Alisabatu ma ta yi cikin ɗa namiji da tsufanta, wannan kuwa shi ne watanta na shaida, ita da ake ce wa bakararriya.

37. Ba wata faɗar Allah da za ta kasa cika.”

38. Sai Maryamu ta ce, “To, ga shi, ni baiwar Ubangiji ce, yă zama mini yadda ka faɗa.” Sai mala'ikan ya tashi daga gare ta.

39. A kwanakin nan Maryamu ta tashi da hanzari, ta tafi wata ƙasa mai duwatsu, zuwa wani gari na ƙasar Yahuza.

40. Ta shiga gidan Zakariya ta gai da Alisabatu.

41. Sai ya zamana da Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, jariri ya motsa da ƙarfi a cikinta. Aka kuwa cika Alisabatu da Ruhu Mai Tsarki,

42. har ta tā da murya da ƙarfi, ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata, ɗan cikinki kuma mai albarka ne!

43. Ta yaya wannan alheri ya same ni, har da uwar Ubangijina za ta zo gare ni?

44. Domin kuwa da jin muryarki ta gaisuwa a kunnena, sai jaririn ya motsa da ƙarfi a cikina domin farin ciki.

45. Albarka tā tabbata ga wadda ta gaskata, domin za a cika abubuwan da Ubangiji ya aiko a faɗa mata.”

46. Sai Maryamu ta ce,“Zuciyata na ɗaukaka shi, Ubangiji,

47. Allah Mai Cetona, da shi ruhuna yake ta farin ciki,

48. Domin fa shi ya dubi ƙasƙancin baiwa tasa.Ga shi, jama'a ta dukan zamanai,Za su ce mini mai albarka ce nan gaba.

49. Domin fa shi da yake Mai Iko,Manyan al'amura ya yi mini,Sunansa labudda mai tsarki ne.

50. Daga zamanai ya zuwa wani zamani,Jinƙansa yana ga waɗanda suke tsoronsa.

51. Manyan ayyuka da ya yi,Masu girmankai, su da dabarbarunsu ya warwatsa.

Karanta cikakken babi Luk 1