Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Kol 4:6-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. A kullum maganarku ta zama mai ƙayatarwa, mai daɗin ji, domin ku san irin amsar da ta dace ku ba kowa.

7. Tikikus zai sanar da ku duk abin da nake ciki. Shi ƙaunataccen ɗan'uwa ne, amintaccen mai hidima, abokin bautarmu kuma a cikin Ubangiji.

8. Na aiko shi a gare ku musamman, domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa muku zuciya.

9. Ga kuma Unisimas a nan tare da shi, amintaccen ɗan'uwa ƙaunatacce, wanda shi ma a cikinku yake. Su za su gaya muku duk abin da ya faru a nan.

10. Aristarkus, abokin ɗaurina, yana gaishe ku, haka kuma Markus, wanda kakansu ɗaya ne da Barnaba. Shi ne aka riga aka yi muku umarni a game da shi. In dai ya zo wurinku, ku karɓe shi.

11. Yasuwa kuma da ake kira Yustus yana gaishe ku. Wato, cikin abokan aikina ga Mulkin Allah, waɗannan su kaɗai ne daga cikin Yahudawa masu bi, sun kuwa sanyaya mini zuciya.

Karanta cikakken babi Kol 4