Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Kol 4:12-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Abafaras wanda yake ɗaya daga cikinku, bawan Almasihu Yesu, yana gaishe ku, a kullum yana yi muku addu'a da himma, ku dage, kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.

13. Na shaide shi, lalle ya yi muku aiki ƙwarai da gaske, da kuma waɗanda suke na Lawudikiya da na Hirafolis.

14. Luka, ƙaunataccen likitan nan, da Dimas suna gaishe ku.

15. A gayar mini da 'yan'uwa na Lawudikiya, da kuma Nimfa da ikilisiyar da take taruwa a gidanta.

16. Sa'ad da aka karanta wasiƙar nan a gabanku, ku sa a karanta ta kuma a gaban ikilisiyar da take a Lawudikiya, ku kuma ku karanta tasu, wato ta Lawudikiyawa.

17. Ku kuma faɗa wa Arkibus ya mai da hankali ya cika hidimar da Ubangiji ya sa shi.

18. Ni Bulus, ni nake rubuta gaisuwar nan da hannuna. Ku tuna da ɗaurina. Alheri yă tabbata a gare ku.

Karanta cikakken babi Kol 4