Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 5:22-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Albarkar Ruhu kuwa ita ce ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci,

23. da tawali'u da kuma kamunkai. Masu yin irin waɗannan abubuwa, ba dama shari'a ta kama su.

24. Waɗanda kuwa suke su na Almasihu Yesu ne, sun gicciye halin mutuntaka da mugayen sha'awace-sha'awace iri iri.

25. In dai rayuwar tamu ta Ruhu ce, to, sai mu tafiyar da al'amuranmu ta wurin ikon Ruhu.

26. Kada mu zama masu homa, muna tsokanar juna, muna yi wa juna hassada.

Karanta cikakken babi Gal 5