Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 3:19-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. To, mece ce manufar Shari'a? Ƙari aka yi da ita don fitowa da laifi fili, har kafin na zuriyar nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin, an kuma ba da ita ta wurin mala'iku ne, ta hannun matsakanci.

20. Matsakanci fa ba domin ɗaya ba ne. Amma Allah ɗaya yake.

21. Wato, Shari'a ta zama saɓanin alkawaran Allah ke nan? A'a, ko kusa! Domin da an ba da wata shari'a mai iya ba da rai, da sai a sami adalcin Allah ta hanyar bin Shari'ar nan.

22. Amma Nassi ya kulle kowa a cikin zunubi, don albarkar da aka yi alkawari saboda gaskatawa da Yesu Almasihu, a ba da ita ga masu ba da gaskiya.

23. Tun kafin bangaskiya ta zo, a cikin ƙangin Shari'a muke a kulle, sai a lokacin da bangaskiya ta bayyana.

24. Ashe kuwa, Shari'a ta zama uwargijiyarmu da ta kai mu ga Almasihu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta wurin bangaskiya.

25. A yanzu kuwa da bangaskiya ta zo, ba sauran zamanmu a hannun wata uwargijiya.

26. Domin dukanku 'ya'yan Allah ne, ta wurin bangaskiya ga Almasihu Yesu.

27. Duk ɗaukacinku da aka yi wa baftisma ga bin Almasihu, kun ɗauki halin Almasihu ke nan.

28. Ba sauran cewa Bayahude ko Ba'al'umme, ko ɗa, ko bawa, ko namiji ko mace. Ai, dukkanku ɗaya kuke, na Almasihu Yesu.

29. In kuwa ku na Almasihu ne, ashe, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda ne kuma bisa ga alkawarin nan.

Karanta cikakken babi Gal 3