Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 3:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ɗauke hankalinku? Ku da aka bayyana muku Yesu Almasihu gicciyeyye sosai.

2. Abu ɗaya kaɗai zan tambaye ku. Kun sami Ruhu saboda bin Shari'a ne, ko kuwa saboda gaskatawa ga maganar da kuka ji?

3. Ashe, rashin azancinku har ya kai ga haka? Da kuka fara da Ruhu, ashe, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa?

4. Ashe, a banza kuka sha wuya iri iri? In dai har a banzan ne!

5. Wato, shi da yake yi muku baiwar Ruhu, yake kuma yin mu'ujizai a cikinku, saboda kuna bin Shari'a ne yake yin haka, ko kuwa saboda gaskatawa da maganar da kuka ji?

6. Haka ma Ibrahim “ya gaskata Allah, bangaskiyan nan tasa kuma, aka lasafta ta adalci ce a gare shi.”

7. Wato kun ga ashe, masu bangaskiya su ne 'ya'yan Ibrahim.

8. A cikin Nassi kuwa an hango, cewa Allah zai kuɓutar da al'ummai ta wurin bangaskiya, wato, dā ma can an yi wa Ibrahim bishara cewa, “Ta wurinka za a yi wa dukkan al'ummai albarka.”

Karanta cikakken babi Gal 3