Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Filib 1:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Bulus da Timoti, bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan tsarkaka a cikin Almasihu Yesu waɗanda suke a Filibi, tare da masu kula da ikkilisiya da kuma masu hidimarta.

2. Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu, su tabbata a gare ku.

3. Ina gode Allahna duk sa'ad da nake tunawa da ku,

4. a kullum kuwa a kowace addu'a da nake muku duka, da farin ciki nake yi.

5. Ina godiya saboda tarayyarku da ni wajen yaɗa bishara, tun daga ranar farko har ya zuwa yanzu.

Karanta cikakken babi Filib 1