Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 7:42-57 Littafi Mai Tsarki (HAU)

42. Saboda haka Allah ya juya musu baya, ya sallame su ga bautar taurari, yadda yake a rubuce a littafin annabawa cewa,‘Ya ku jama'ar Isra'ila,Ni ne kuka yanka wa dabbobi, kuka miƙa wa hadaya,Har shekara arba'in a cikin jeji?

43. Ai, yawo kuka yi da alfarwar Molek,Da surar tauraron gunki Ramfan,Wato surorin nan da kuka ƙera don ku yi musu sujada.Ni kuwa zan kawar da ku a can bayan Babila.’

44. “Dā kakanninmu suna da alfarwar shaida a jeji, irin wadda mai maganar nan da Musa ya umarta a yi, daidai fasalin da ya gani.

45. Alfarwan nan ita ce kakanninmu suka gāda, suka kuma kawo ƙasar nan a zamanin Joshuwa, bayan sun mallake ƙasar al'umman da Allah ya kora a gaban idonsu. Alfarwan nan kuwa tana nan har ya zuwa zamanin Dawuda,

46. wanda ya sami tagomashi wurin Allah, har ya nemi alfarmar yi wa Allahn Yakubu masujada.

47. Amma Sulemanu ne ya yi wa Allah gini.

48. Duk da haka Maɗaukaki ba ya zama a gidaje, ginin mutum. Yadda Annabi Ishaya ya ce,

49. ‘Allah ya ce, Sama ita ce kursiyina,Ƙasa kuwa matashin ƙafata.Wane wuri kuma za ku gina mini?Ko kuwa wane wuri ne wurin hutuna?

50. Ba da ikona na halicci dukan waɗannan abubuwa ba?’

51. “Ku kangararru, masu ɓatan basira, masu kunnen ƙashi, kullum kuna yi wa Ruhu Mai Tsarki tsayayya. Yadda kakanninku suka yi, haka ku ma kuke yi.

52. A cikin annabawa wane ne kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun kuma kashe waɗanda suka yi faɗi a kan zuwan Mai Adalcin nan, wanda a yanzu kuka zama maciya amanarsa, da kuma makasansa,

53. ku ne kuwa kuka karɓi Shari'a ta wurin mala'iku, amma ba ku kiyaye ta ba!”

54. Da suka ji haka, suka husata ƙwarai da gaske, har suka ciji baki don jin haushinsa.

55. Amma Istifanas, a cike da Ruhu Mai Tsarki, sai ya zuba ido sama, ya ga ɗaukakar Allah, da kuma Yesu tsaye a dama ga Allah.

56. Sai ya ce, “Ga shi, ina ganin sama a buɗe, da kuma Ɗan Mutum tsaye dama ga Allah.”

57. Amma suka ɗauki ihu ƙwarai, suka tattoshe kunnuwansu, suka aukar masa da nufi ɗaya,

Karanta cikakken babi A.m. 7