Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 4:20-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Domin mu kam, ba yadda za a yi sai mun faɗi abin da muka ji, muka kuma gani.”

21. Da kuma suka daɗa yi musu kashedi, suka sake su, don sun rasa yadda za su hore su saboda jama'a, domin dukan mutane suna ɗaukaka Allah saboda abin da ya auku.

22. Mutumin nan da aka yi wa mu'ujizar nan ta warkarwa kuwa ya ba shekara arba'in baya.

23. Da aka sau su, suka tafi wurin mutanensu, suka ba su labarin duk abin da manyan firistoci da shugabanni suka faɗa musu.

24. Su kuwa da jin haka, sai suka ɗaga muryarsu ga Allah da nufi ɗaya, suka ce, “Ya Mamallaki, Mahaliccin sama, da ƙasa, da teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu,

25. wanda ta Ruhu Mai Tsarki, ta bakin kakanmu Dawuda baranka, ka ce,‘Don me al'ummai suka husata?Kabilai kuma suka yi makidar al'amuran wofi?

26. Sarakunan duniya sun kafa dāga,Mahukunta kuma sun haɗa kai,Suna gāba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.’

27. Gama hakika Hirudus da Buntus Bilatus sun haɗa kai a birnin nan tare da al'ummai da jama'ar Isra'ila gāba da Yesu Baranka mai tsarki, wanda ka maishe shi Almasihu.

28. Sun haɗa kai domin su yi dukan abin da ka ƙaddara zai auku, bisa ga ikonka da nufinka.

29. Yanzu kuma ya Ubangiji, dubi wannan kashedin nasu, ka yi wa bayinka baiwar yin maganarka da iyakar ƙarfin hali,

30. kana kuma miƙo hannunka kana warkarwa, ana kuma yin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi albarkacin sunan Baranka mai tsarki Yesu.”

31. Bayan sun yi addu'a, wurin da suke a tattare ya raurawa. Sai duk aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta faɗar maganar Allah gabagaɗi.

32. To, duk taron da suka ba da gaskiya kuwa nufinsu ɗaya ne, ra'ayinsu ɗaya, ba kuma waninsu da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, sai dai kome nasu ne baki ɗaya.

33. Manzanni kuma suka yi shaida da tabbatarwa mai ƙarfi a kan tashin Ubangiji Yesu daga matattu. Alheri mai yawa yana tare da kowannensu,

34. har ba wanda yake da rashi a cikinsu ko ɗaya, don duk masu gonaki ko gidaje sun sayar da su,

35. sun kawo kuɗin, sun ajiye gaban manzanni, an kuwa rarraba wa kowa gwargwadon bukatarsa.

36. Ana cikin haka sai Yusufu, wani Balawiye, asalinsa mutumin tsibirin Kubrus, wanda manzannin suke kira Barnaba, (wato ɗan ƙarfafa zuciya),

37. ya sayar da wata gonarsa, ya kawo kuɗin ya ajiye a gaban manzannin.

Karanta cikakken babi A.m. 4