Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 4:19-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Amma Bitrus da Yahaya suka mayar musu da jawabi suka ce, “To, in daidai ne a gun Allah mu fi jin taku da ta Allah, sai ku duba ku gani.

20. Domin mu kam, ba yadda za a yi sai mun faɗi abin da muka ji, muka kuma gani.”

21. Da kuma suka daɗa yi musu kashedi, suka sake su, don sun rasa yadda za su hore su saboda jama'a, domin dukan mutane suna ɗaukaka Allah saboda abin da ya auku.

22. Mutumin nan da aka yi wa mu'ujizar nan ta warkarwa kuwa ya ba shekara arba'in baya.

23. Da aka sau su, suka tafi wurin mutanensu, suka ba su labarin duk abin da manyan firistoci da shugabanni suka faɗa musu.

24. Su kuwa da jin haka, sai suka ɗaga muryarsu ga Allah da nufi ɗaya, suka ce, “Ya Mamallaki, Mahaliccin sama, da ƙasa, da teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu,

25. wanda ta Ruhu Mai Tsarki, ta bakin kakanmu Dawuda baranka, ka ce,‘Don me al'ummai suka husata?Kabilai kuma suka yi makidar al'amuran wofi?

26. Sarakunan duniya sun kafa dāga,Mahukunta kuma sun haɗa kai,Suna gāba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.’

27. Gama hakika Hirudus da Buntus Bilatus sun haɗa kai a birnin nan tare da al'ummai da jama'ar Isra'ila gāba da Yesu Baranka mai tsarki, wanda ka maishe shi Almasihu.

Karanta cikakken babi A.m. 4