Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 4:11-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Wannan shi ne dutsen nan da ku magina kuka raina, shi ne kuwa ya zama mafificin dutsen gini.

12. Ba kuma samun ceto ga wani, domin ba wani suna duk duniyan nan da aka bayar cikin mutane, wanda lalle ta wurinsa ne za mu sami ceto.”

13. To, da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yahaya, suka kuma gane marasa ilimi ne, talakawa kuma, suka yi mamaki, suka kuwa shaida su, a kan dā suna tare da Yesu.

14. Amma da suka ga mutumin nan da aka warkar ɗin yana tsaye tare da su, suka rasa hanyar yin mūsu.

15. Bayan sun umarce su, su fita daga majalisa, suka yi shawara da juna,

16. suka ce, “Yaya za mu yi da mutanen nan? Don hakika sanannen abu ne ga dukan mazauna Urushalima, cewa an yi wata tabbatacciyar mu'ujiza ta wurinsu, ba mu kuwa da halin yin mūsawa.

17. Amma don kada abin ya ƙara bazuwa a cikin mutane, sai mu yi musu kashedi, kada su kuskura su ƙara yi wa kowa magana, suna kama wannan suna.”

18. Sai suka kirawo manzannin, suka kwaɓe su, kada su kuskura su yi wa kowa magana, ko su ƙara koyarwa suna kama sunan Yesu.

19. Amma Bitrus da Yahaya suka mayar musu da jawabi suka ce, “To, in daidai ne a gun Allah mu fi jin taku da ta Allah, sai ku duba ku gani.

20. Domin mu kam, ba yadda za a yi sai mun faɗi abin da muka ji, muka kuma gani.”

Karanta cikakken babi A.m. 4