Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 3:17-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. “To, yanzu 'yan'uwa, na sani da jahilci kuka yi haka, kamar yadda shugabanninku ma suka yi.

18. Amma ta haka Allah ya cika faɗar da ya riga ya yi ta bakin annabawa duka, cewa Almasihunsa zai sha wuya.

19. Saboda haka sai ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, Ubangiji kuma kansa ya riƙa wartsakar da ku,

20. ya kuma aiko da Almasihun da aka ƙaddara muku tun dā, wato Yesu,

21. wanda lalle ne ya zauna a Sama, har kafin lokacin nan na sabunta dukkan abubuwa da Allah ya faɗa tun zamanin dā ta bakin annabawansa tsarkaka.

22. Musa ma ya ce, ‘Ubangiji Allah zai tasar muku da wani annabi daga cikin 'yan'uwanku, kamar yadda ya tashe ni. Lalle ne ku saurari duk abin da ya faɗa muku.

23. Zai zamana kuma duk wanda ya ƙi sauraron annabin nan, za a hallaka shi daga cikin jama'a.’

24. Hakika dukan annabawa da suka yi annabci, wato tun daga kan Sama'ila da waɗanda suka zo daga baya, duk sun yi faɗi a kan waɗannan kwanakin.

25. Ku ne tsatson annabawa, ku ne kuma magadan alkawarin da Allah ya yi wa kakanninku, da ya ce wa Ibrahim, ‘Ta zuriyarka ne za a yi wa dukkan kabilan duniya albarka.’

26. Da Allah ya taso da Baransa, gare ku ne ya fara aiko shi, don yă yi muku albarka ta juyo da ko wannenku ga barin muguntarsa.”

Karanta cikakken babi A.m. 3