Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 3:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, Bitrus da Yahaya suna tafiya Haikali a lokacin addu'a, da ƙarfe uku na yamma,

2. sai ga wani mutum da aka haifa gurgu, ana ɗauke da shi. Kowace rana kuwa akan ajiye shi a ƙofar Haikali, wadda ake kira Ƙawatacciyar Ƙofa, don ya roƙi sadaka ga masu shiga Haikali.

3. Da ganin Bitrus da Yahaya suna shiga Haikalin, ya roƙe su sadaka.

4. Bitrus kuwa ya zuba masu ido, tare da Yahaya, ya ce, “Dube mu.”

5. Sai kuwa duk hankalinsa ya koma a kansu, da tsammanin samun wani abu a gunsu.

6. Amma Bitrus ya ce, “Kuɗi kam, ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka. Da sunan Yesu Almasihu Banazare, yi tafiya.”

7. Sai Bitrus ya kama hannunsa na dama, ya tashe shi. Nan tāke ƙafafunsa da wuyan sawunsa suka yi ƙarfi.

8. Wuf, sai ya zabura, ya miƙe tsaye, ya fara tafiya, ya shiga Haikalin tare da su, yana tafe, yana tsalle, yana kuma yabon Allah.

9. Duk mutane suka gan shi yana tafe yana yabon Allah.

10. Suka kuwa gane shi ne mai zama a bakin Ƙawatacciyar Ƙofa ta Haikali yana bara. Sai mamaki ya kama su, suna al'ajabi ƙwarai a kan abin da aka yi masa.

11. Tun yana riƙe da Bitrus da Yahaya, duk jama'a suka sheƙa a guje zuwa wurinsu a cikin shirayin da ake kira Shirayin Sulemanu, suka ruɗe don mamaki.

12. Da Bitrus ya ga haka, sai ya yi wa jama'a jawabi, ya ce, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, don me kuke mamakin wannan? Don me kuma kuke ta dubanmu, sai ka ce da ikon kanmu ne, ko kuwa don ibadarmu muka sa shi tafiya?

13. Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allahn kakanninmu, shi ya ɗaukaka Baransa Yesu, wanda kuka bashe shi, kuka kuma ƙi shi, a gaban Bilatus, sa'ad da ya ƙudura zai sake shi.

Karanta cikakken babi A.m. 3