Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 27:41-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

41. Amma da muka isa wata mahaɗar ruwa, sai suka tura jirgin ya dunguri yashi, har goshinsa ya cije ya kasa motsi, ƙarshensa kuma ya fara ragargejewa saboda haukan raƙuman ruwa.

42. Sai sojan suka yi niyya su kashe 'yan sarka, don kada wani ya yi ninƙaya ya tsira.

43. Amma jarumin da ya so ya ceci Bulus, ya hana i da nufinsu, ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci,

44. sauran kuwa waɗansu suka hau katako, waɗansu kuma suka hau tarkacen jirgin. Da haka duk suka kai gaci lafiya.

Karanta cikakken babi A.m. 27