Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 27:28-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Sai suka gwada zurfin ruwan, suka sami gaba ashirin, da muka ci gaba kaɗan, sai suka sāke gwadawa, suka sami gaba goma sha biyar.

29. Don gudun kada a fyaɗa mu a kan duwatsu, sai suka saki anka guda huɗu na bayan jirgin, suka ƙagauta gari ya waye.

30. Masu tuƙi suna neman gudu daga jirgin ke nan, har sun zura ƙaramin jirgi a cikin ruwa, wai don a ga kamar za su ja su anka ɗin ne daga goshin jirgin su sake su,

31. sai Bulus ya ce da jarumin yaki da kuma sojan. “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba yadda za a yi ku tsira.”

32. Sai sojan suka yayyanke igiyoyin ƙaramin jirgin, suka bar shi ya bi ruwa.

33. Da gari ya yi kusan wayewa sai Bulus ya roƙe su su taɓa ɗan abinci, ya ce, “Yau fa kwana goma sha huɗu ke nan kuke zaman jira, ba wani abin da kuka ci.

34. Saboda haka, ina roƙonku ku ci abinci, don lafiyarku, tun da yake ba wanda ko gashin kansa zai yi ciwo a cikinku.”

35. Da ya faɗi haka, ya ɗauki curin gurasa, ya yi godiya ga Allah a gabansu duka, sa'an nan ya gutsuttsura ya fara ci.

36. Sai duk suka farfado, su ma kansu suka ci abinci.

37. Mu duka a cikin jirgin kuwa mutum metan da saba'in da shida ne.

38. Da suka ci suka ƙoshi, sai suka riƙa rage wa jirgin nauyi, suka yi ta zub da alkama a cikin ruwa.

39. Da gari ya waye ba su shaida ƙasar ba, amma dai sun lura da wani lungu da gaci mai yashi, sai kuma suka yi shawara cewa in mai yiwuwa ne su kai jirgin kan yashin.

40. Sai suka daddatse su anka duka, suka bar su a ruwa, suna kuma ɓalle maɗaurin abin juyar da jirgin a lokacin, sa'an nan kuma suka ta da filafilan goshin jirgin daidai iska, suka doshi gaci.

41. Amma da muka isa wata mahaɗar ruwa, sai suka tura jirgin ya dunguri yashi, har goshinsa ya cije ya kasa motsi, ƙarshensa kuma ya fara ragargejewa saboda haukan raƙuman ruwa.

Karanta cikakken babi A.m. 27