Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 26:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga nan, sai Agaribas ya ce wa Bulus, “An ba ka izinin yin magana.”Sa'an nan fa Bulus ya ɗaga hannu, ya fara kawo hanzarinsa ya ce,

2. “Lalle na yi arziki, ya sarki Agaribas, da yake a gabanka ne zan kawo hanzarina yau a game da duk ƙarata da Yahudawa suka yi,

3. musamman da yake gwani ne kai ga sanin al'adun Yahudawa da maganganunsu. saboda haka, ina roƙonka ka saurare ni da haƙuri.

4. “Irin zaman da na yi tun daga ƙuruciyata, wato tun da farko, a cikin jama'armu da kuma a Urushalima har ya zuwa yau, sananne ne ga dukan Yahudawa.

5. Sun sani tun ainihi, in dai za su yarda su yi shaida, cewa lalle ni Bafarisiye ne bisa ga ɗariƙar nan da ta fi tsanani cikin addinin nan namu.

6. Ai, saboda na sa zuciya ga cikar alkawarin nan ne da Allah ya yi wa kakanninmu nake nan a tsaye a yi mini shari'a.

7. Alkwarin nan kuwa, shi ne wanda kabilanmu goma sha biyu suke himmantuwa ga bauta wa Allah dare da rana, suna sa zuciya su ga cikarsa. Saboda sa zuciyar nan kuma fa Yahudawa suke ƙarata, ya sarki!

8. Yaya cewa Allah yana ta da matattu sa'an nan, ya ƙi gaskatuwa a gare ku?

9. “To, ni kaina ma a dā na ga kamar wajibi ne in yi abubuwa da yawa, na gāba da sunan Yesu Banazare.

10. Na kuwa yi haka a Urushalima, har na sami izini daga manyan firstoci, na kulle tsarkaka da yawa a kurkuku. Har ma a lokacin da ake kashe su ina goyon bayan yin haka.

11. Na kuma sha gwada musu azaba a dukan majami'u, ina ƙoƙarin sa su yin saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.”

Karanta cikakken babi A.m. 26