Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 25:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma Bulus ya kawo hanzarinsa ya ce, “Ni ban yi wani laifi game da shari'ar Yahudawa, ko Haikali, ko a game da Kaisar ba, ko kaɗan.”

9. Festas kuwa don neman farin jini wurin Yahudawa, ya amsa ya ce wa Bulus, “Ka yarda ka je Urushalima a yi maka shari'a a can a kan waɗannan abubuwa a gabana?”

10. Amma Bulus ya ce, “Ai, a tsaye nake a majalisar Kaisar, a inda ya kamata a yi mini shari'a. Ban yi wa Yahudawa wani laifi ba, kai kanka kuwa ka san da haka sarai.

11. To, in ni mai laifi ne, har na aikata abin da ya isa kisa, ai, ba zan guji a kashe ni ba, amma in ba wata gaskiya a cikin ƙarata da suke yi, to, ba mai iya bashe ni gare su don a faranta musu rai. Na nema a ɗaukaka ƙarata gaban Kaisar.”

12. Bayan da Festas ya yi shawara da majalisa, sai ya amsa ya ce, “To, ka nema a ɗaukaka ƙararka gaban Kaisar! Gun Kaisar kuwa za ka tafi.”

13. Bayan 'yan kwanaki sai sarki Agaribas da Barniki, suka zo Kaisariya don su yi wa Festas maraba.

14. Da yake kuma sun yi kwanaki da dama a can, sai Festas ya rattaba wa sarki labarin Bulus, ya ce, “Akwai wani mutumin da Filikus ya bari a ɗaure,

15. wanda sa'ad da nake Urushalima manyan firistoci da shugabannin Yahudawa suka kawo mini ƙararsa, suka roƙe ni in yi masa hukunci.

16. Ni kuwa na amsa musu na ce, ba al'adar Romawa ba ce a yi wa wani hukunci, don faranta wa wani rai, ba tare da masu ƙarar, da wanda aka kai ƙara, sun kwanta a gaban shari'a ba, ya kuma sami damar kawo hanzarinsa game da ƙarar da aka tāsar.

17. Saboda haka, da suka zo nan tare, ban yi wani jinkiri ba, sai kawai na hau gadon shari'a kashegari, na kuma yi umarni a kawo mutumin.

18. Da masu ƙarar suka tashi tsaye, ba su kawo wata mummunar ƙara yadda na zata a game da shi ba,

Karanta cikakken babi A.m. 25