Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 24:22-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Filikus kuwa da yake yana da sahihin ilimi a game da wannan hanya ya dakatar da su, ya ce, “In shugaba Lisiyas ya iso, zan yanke muku shari'a.”

23. Ya kuma ba jarumi umarni ya tsare Bulus, amma ya sassauta masa, kada kuwa ya hana mutanensa zuwa wurinsa su kula da shi.

24. Bayan 'yan kwanaki Filikus ya zo tare da matarsa, Durusila, wata Bayahudiya. Sai ya aika a zo da Bulus, ya kuwa saurare shi a kan maganar gaskatawa da Almasihu Yesu.

25. Bulus yana ba da bayani a kan adalci, da kamunkai, da kuma hukuncin nan mai zuwa, Filikus ya kaɗu, ya kāda baki ya ce, “Yanzu kam, sai ka koma. In na sami zarafi nā kira ka.”

26. Don yana sa rai Bulus zai ba shi kuɗi, shi ya sa ya yi ta kiransa a kai a kai, yana zance da shi.

27. Amma bayan shekara biyu sai Borkiyas Festas ya gāji Filikus. Filikus kuwa don neman farin jini a wurin Yahudawa, ya bar Bulus a ɗaure.

Karanta cikakken babi A.m. 24