Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 23:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sai Bulus ya ce masa, “Kai munafiƙi, kai ma Allah zai buge ka! Ashe, wato kana zaune kana hukunta ni bisa ga Shari'a ne, ga shi kuwa kana yin umarni a doke ni, a saɓanin Shari'a?”

4. Sai waɗanda suke tsaye a wurin suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?”

5. Sai Bulus ya ce, “Ai, ban sani shi ne babban firist ba, 'yan'uwa, don a rubuce yake cewa, ‘Kada ka munana shugaban jama'a.’ ”

6. Amma da Bulus ya ga sashe ɗaya Sadukiyawa ne, ɗayan kuma Farisiyawa, ya ɗaga murya a majalisar ya ce, “Ya 'yan'uwa, ni ma Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ga shi kuwa, saboda na sa zuciya ga tashin matattu ne ake yi mini shari'a.”

7. Da ya faɗi haka sai gardama ta tashi a tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, har taron ya rabu biyu.

8. Sadukiyawa sun ce, wai ba tashin matattu, ba kuma mala'iku, ko ruhu. Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.

Karanta cikakken babi A.m. 23