Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 23:17-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Bulus kuwa ya kira wani jarumi ya ce, “Ka kai saurayin nan wurin shugaba, yana da wata magana da zai faɗa masa.”

18. Sai jarumin ya ɗauki saurayin ya kai shi gun shugaba, ya ce, “Ɗan sarƙan nan, Bulus, ya kira ni, ya roƙe ni in kawo saurayin nan a wurinka, don yana da wata maganar da zai gaya maka.”

19. Sai shugaban ya kama hannun saurayin, ya ja shi a waje ɗaya, ya tambaye shi a keɓance, “Wace magana za ka gaya mini?”

20. Yaron ya ce, “Yahudawa sun ƙulla za su roƙe ka ka kai musu Bulus majalisa gobe, kamar suna so su ƙara bincika maganarsa sosai.

21. Amma kada ka yardar musu, don fiye da mutum arba'in daga cikinsu suna fakonsa, sun kuma yi rantsuwa a kan ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kashe shi. Yanzu kuwa a shirye suke, yardarka kawai suka jira.”

22. Sai shugaban ya sallami saurayin ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa cewa ka sanar da ni maganar nan.”

23. Sa'an nan ya kira jarumi biyu ya ce, “Ku shirya soja metan, da barade saba'in, da 'yan māsu metan, su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan.”

24. Ya kuma yi umarni su shirya wa Bulus dabbobin da zai hau, don su kai shi wurin mai mulki Filikus lafiya.

25. Ya kuma rubuta wasiƙa kamar haka:

26. “Daga Kalaudiyas Lisiyas zuwa ga mafifici mai mulki Filikus. Gaisuwa mai yawa.

27. Bayan haka mutumin nan, Yahudawa sun kama shi, suna kuma gab da kashe shi, sai na yi farat na je da soja na ƙwato shi, saboda na ji cewa shi Barome ne.

28. Da ina so jin laifin da suke zarginsa a kai, sai na kai shi majalisarsu.

29. Na kuwa tarar suna zarginsa a kan maganar Shari'arsu, amma laifin da suka ɗora masa bai kai ga kisa ko ɗauri ba.

Karanta cikakken babi A.m. 23