Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 22:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ya ku 'yan'uwa da shugabanni, ku ji hanzarin da zan kawo muku a yanzu.”

2. Da suka ji ya yi musu magana da Yahudanci, sai suka ƙara natsuwa. Sa'an nan ya ce,

3. “Ni bayahude ne, haifaffen Tarsus, ƙasar Kilikiya, amma a nan garin na girma, aka kuma karantar da ni wurin Gamaliyal, bisa ga tsarin tsanantacciyar hanyar nan ta Shari'ar kakanninmu. Ina mai himmar bauta wa Allah, kamar yadda dukanku kuke a yau,

4. har na tsananta wa masu bin wannan hanya, ina karkashe su, ina ɗaure mutane maza da mata, ina jefa su a kurkuku.

5. Babban firist ma da dukan majalisar shugabannin jama'a za su iya shaidata, daga gunsu ne kuma na karɓi wasiƙu zuwa ga 'yan'uwanmu Yahudawa, na tafi Dimashƙu, don in ɗebo waɗanda suke can ma, in zo da su Urushalima a ɗaure, a azabta su.”

6. “Ina cikin tafiya, da na yi kusa da Dimashƙu, wajen rana tsaka, kwamfa sai wani matsanancin haske ya bayyano daga sama, ya haskaka kewaye da ni.

7. Sai na fāɗi, na kuma ji wata murya tana ce mini, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?’

8. Ni kuma na amsa na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ Sai ya ce mini, ‘Ni ne Yesu Banazare wanda kake tsananta wa.’

Karanta cikakken babi A.m. 22