Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 21:32-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. A nan tāke ya ɗibi soja da jarumawa, suka ruga zuwa wajensu. Su kuwa da ganin shugaban da soja suka daina dūkan Bulus.

33. Sai shugaban ya matsa kusa ya kama Bulus, ya yi umarni a ɗaure shi da sarƙa biyu, sa'an nan ya tambaya ko shi wane ne, da abin da kuma ya yi.

34. Taron kuwa suka ɗau kururuwa, waɗansu suka ce kaza, waɗansu suka ce kaza. Don tsananin hargowa ma har ya kasa samun ainihin tushen maganar, ya yi umarni a kai shi kagarar sojoji.

35. Da Bulus ya zo ga bakin matakala, sai da soja suka kinkime shi saboda haukan taron,

36. don taron jama'a na dannowa a bayansu, suna ihu suna cewa, “A yi da shi!”

37. An yi kusan shigar da Bulus kagarar sojoji ke nan, sai ya ce wa shugaban, “Ko ka yarda in yi magana da kai?” Sai shugaban ya ce, “Ashe, ka iya Helenanci?

38. Shin, ba kai ne Bamasaren nan da shekarun baya ya haddasa tawaye ba, har ya ja mutanen nan dubu huɗu masu kisankai jeji?”

39. Sai Bulus ya amsa ya ce, “Ai, ni Bayahude ne na Tarsus ta ƙasar Kilikiya, ɗan shahararren birni, ina roƙonka ka bar ni in yi wa mutane jawabi.”

40. Da ya ba shi izini, sai Bulus ya tsaya a kan matakala, ya ɗaga wa jama'a hannu su yi shiru. Da suka yi tsit, sai ya yi musu magana da Yahudanci.

Karanta cikakken babi A.m. 21