Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 20:16-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Dā ma kuwa Bulus ya ƙudura zai wuce Afisa cikin jirgin, don kada ya yi jinkiri a Asiya, domin yana sauri, in mai yiwuwa ne ma, ya kai Urushalima a ranar Fentikos.

17. Daga Militas ne ya aika Afisa a kira masa dattawan Ikkilisiya.

18. Da suka zo wurinsa sai ya ce musu, “Ku da kanku kun san irin zaman da na yi a cikinku, tun ran da na sa ƙafata a ƙasar Asiya,

19. ina bauta wa Ubangiji da matuƙar tawali'u, har da hawaye, da gwaggwarmaya iri iri da na sha game da makircin Yahudawa.

20. Kun kuma san yadda ban ji nauyin sanar da ku kowane abu mai amfani ba, ina koya muku a sarari, da kuma gida gida,

21. ina tabbatar wa Yahudawa da al'ummai duka sosai wajibcin tuba ga Allah, da kuma gaskatawa da Ubangijinmu Yesu.

22. To, ga shi kuma, yanzu zan tafi Urushalima, Ruhu yana iza ni, ban kuwa san abin da zai same ni a can ba,

23. sai dai Ruhu Mai Tsarki yakan riƙa tabbatar mini a kowane gari, cewa ɗauri da shan wuya na dākona.

24. Amma ni ban mai da raina a bakin kome ba, bai kuma dame ni ba, muddin zan iya cikasa tserena da kuma hidimar da na karɓa gun Ubangiji Yesu, in shaidar da bisharar alherin Allah.

25. To, ga shi, yanzu na san dukanku ba za ku ƙara ganina ba, ku da na zazzaga cikinku ina yi muku bisharar Mulkin Allah.

26. Saboda haka ina dai tabbatar muku a yau, cewa na kuɓuta daga hakkin kowa,

27. domin ban ji nauyin sanar da ku dukan nufin Allah ba.

28. Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.

Karanta cikakken babi A.m. 20