Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 2:9-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ga mu kuwa, Fartiyawa, da Madayanawa, da Elamawa, da mutanen ƙasar Bagadaza, da na Yahudiya, da na Kafadokiya, da na Fantas, da na Asiya,

10. da na Firijiya, da na Bamfiliya, da na Masar, da kuma na kewayen Kurane ta ƙasar Libiya, har ma da baƙi daga Roma, wato Yahudawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci,

11. da kuma Karitawa, da Larabawa, duk muna ji suna maganar manyan al'amuran Allah da bakunan garuruwanmu.”

12. Duk kuwa suka yi mamaki, suka ruɗe, suna ce wa juna, “Me ke nan kuma?”

13. Amma waɗansu suka yi ba'a suka ce, “Ruwan inabi suka sha suka yi tatul!”

14. Amma Bitrus ya miƙe tare da sha ɗayan nan, ya ɗaga murya ya yi musu jawabi, ya ce, “Ya ku 'yan'uwana Yahudawa da dukan mazaunan Urushalima, ku kula da wannan, ku kuma saurari maganata.

15. Ai, mutanen nan ba bugaggu ba ne yadda kuke zato, tun da yake yanzu ƙarfe tare na safe ne kawai.

16. Wannan, ai, shi ne abin da Annabi Yowel ya faɗa cewa,

17. ‘Allah ya ce,A zamanin karshe zai zamanto zan zubo wa dukan 'yan adam Ruhuna.'Ya'yanku mata da maza za su yi annabci,Wahayi zai zo wa samarinku,Dattawanku kuma za su yi mafarkai.

18. Hakika, har ma a kwanakin nan zan zubo Ruhuna a kan bayina mata da maza,Za su kuma yi annabci.

19. Zan nuna abubuwan al'ajabi a sararin sama,Da mu'ujizai a nan ƙasa,Wato jini, da wuta, da kuma, hauhawan hayaƙi.

20. Za a mai da rana duhu,Wata kuma jini,Kafin Ranar Ubangiji ta zo,Babbar ranar nan mai girma.

21. A sa'an nan ne zai zamanto kowa ya yi addu'a da sunan Ubangiji zai sami ceto.’

22. “Ya ku 'yan'uwa, Isra'ilawa, ku ji wannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar muku cewa shi yardajjensa ne, ta mu'ujizai, da abubuwan al'ajabi, da alamu waɗanda ya yi ta wurinsa a cikinku, kamar yadda ku kanku kuka sani,

23. shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi.

Karanta cikakken babi A.m. 2