Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 19:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Amma da waɗansu suka taurare, suka ƙi ba da gaskiya, suna kushen wannan hanya gaban jama'a, sai ya rabu da su, ya keɓe masu bi, yana ta muhawwara da su a kowace rana makarantar Tiranas.

10. Shekara biyu ana wannan, har dukan mazaunan ƙasar Asiya suka ji Maganar Ubangiji, Yahudawa da al'ummai duka.

11. Ta hannun Bulus kuma Allah ya yi waɗansu mu'ujizai da ba a saba gani ba,

12. har akan kai wa marasa lafiya adikansa, ko tufafinsa da yake sawa yana aiki, sun kuwa warke daga cuce-cucensu, baƙaƙen aljannu kuma sun rabu da su.

13. Sai waɗansu Yahudawa masu yawo gari gari, matsubbata, suka yi ƙoƙarin kama sunan Ubangiji Yesu ga masu baƙaƙen aljannu, suna cewa, “Mun umarce ku da sunan Yesun nan da Bulus yake wa'azi.”

14. To, akwai 'ya'ya bakwai maza, na wani babban firist na Yahudawa, mai suna Siba, duk suna yin wannan abu.

15. Amma aljanin ya amsa musu ya ce, “Yesu dai na san shi, na kuma san Bulus, to, ku kuma ku wane ne?”

16. Mutumin nan mai aljanin sai ya daka tsalle, ya fāɗa musu, ya fi ƙarfinsu dukkansu, ya ci ɗunguminsu, har suka fita daga gidan a guje, a tuɓe, suna masu rauni.

17. Wannan abu fa ya sanu ga dukan mazaunan Afisa, Yahudawa da al'ummai duka, duka kuma tsoro ya kama su, aka kuwa ɗaukaka sunan Ubangiji Yesu.

18. Da yawa kuma daga cikin waɗanda suka ba da gaskiya suka zo, suna bayyana ayyukansu a fili.

Karanta cikakken babi A.m. 19