Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 19:32-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Taron kuwa, waɗansu suka ta da murya su ce kaza, waɗansu su ce kaza, don duk taron a ruɗe yake, yawancinsu ma ba su san dalilin da ya sa suka taru ba.

33. Da Yahudawa suka gabatar da Iskandari, waɗansu suka ɗauka a kan shi ne sanadin abin. Iskandari kuwa ya ɗaga hannu a yi shiru, don ya kawo musu hanzari,

34. amma da suka fahimci, cewa shi Bayahude ne, suka ɗaga murya gaba ɗaya har wajen sa'a biyu, suna cewa, “Girma yā tabbata ga Artimas ta Afisawa!”

35. To, da magatakardan garin ya kwantar da hankalin jama'a, ya ce, “Ku mutanen Afisa! Wane mutum ne bai san cewa musamman birnin Afisawa ne suke kula da haikalin mai girma Artimas ba, da kuma dutsen nan da ya faɗo daga sama?

36. To, da yake ba dama a yi musun waɗannan abubuwa, ai, ya kamata ku natsu, kada ku yi kome da garaje.

37. Ga shi, kun kawo mutanen nan, su kuwa ba su yi sata a ɗakin uwargijiya ba, ba su kuma saɓi uwargijiyarmu ba.

38. To, in Dimitiriyas da abokan sana'arsa suna da wata magana a game da wani, ai, ga ɗakin shari'a a buɗe, ga kuma mahukunta, sai su kai ƙara.

39. Amma in wani abu kuke nema dabam, to, ai, sai a daidaita a majalisa ke nan.

40. Hakika muna cikin hatsarin amsa ƙara a kan tawaye saboda al'amarin nan na yau, tun da yake ba za mu iya ba da wani hanzari game da taron hargitsin nan ba.”

41. Da ya faɗi haka ya sallami taron.

Karanta cikakken babi A.m. 19