Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 19:2-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. sai ya ce musu, “Kun sami Ruhu Mai Tsarki sa'ad da kuka ba da gaskiya?” Suka ce masa, “Ba mu ma ji zuwan Ruhu Mai Tsarki ba.”

3. Sai ya ce, “To, wace baftisma ke nan aka yi muku?” Suka ce, “Irin ta Yahaya ce.”

4. Bulus ya ce, “Ai, Yahaya baftisma ya yi a tuba, yana faɗa wa mutane su gaskata da mai zuwa bayansa, wato Yesu.”

5. Da suka ji haka, aka yi musu baftisma da sunan Ubangiji Yesu.

6. Da Bulus ya ɗora musu hannu, Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu, suka kuwa yi magana da waɗansu harsuna, suna annabci.

7. Su wajen sha biyu ne duka duka.

8. Sai ya shiga majami'a yana wa'azi gabagaɗi, ya kuma yi wata uku yana muhawwara da su, yana kuma rinjayarsu a kan al'amarin Mulkin Allah.

9. Amma da waɗansu suka taurare, suka ƙi ba da gaskiya, suna kushen wannan hanya gaban jama'a, sai ya rabu da su, ya keɓe masu bi, yana ta muhawwara da su a kowace rana makarantar Tiranas.

10. Shekara biyu ana wannan, har dukan mazaunan ƙasar Asiya suka ji Maganar Ubangiji, Yahudawa da al'ummai duka.

11. Ta hannun Bulus kuma Allah ya yi waɗansu mu'ujizai da ba a saba gani ba,

12. har akan kai wa marasa lafiya adikansa, ko tufafinsa da yake sawa yana aiki, sun kuwa warke daga cuce-cucensu, baƙaƙen aljannu kuma sun rabu da su.

13. Sai waɗansu Yahudawa masu yawo gari gari, matsubbata, suka yi ƙoƙarin kama sunan Ubangiji Yesu ga masu baƙaƙen aljannu, suna cewa, “Mun umarce ku da sunan Yesun nan da Bulus yake wa'azi.”

Karanta cikakken babi A.m. 19