Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 19:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, lokacin da Afolos yake Koranti, Bulus ya zazzaga ƙasar ta kan tudu, ya gangara zuwa Afisa. A can ya tarar da waɗansu masu bi,

2. sai ya ce musu, “Kun sami Ruhu Mai Tsarki sa'ad da kuka ba da gaskiya?” Suka ce masa, “Ba mu ma ji zuwan Ruhu Mai Tsarki ba.”

3. Sai ya ce, “To, wace baftisma ke nan aka yi muku?” Suka ce, “Irin ta Yahaya ce.”

4. Bulus ya ce, “Ai, Yahaya baftisma ya yi a tuba, yana faɗa wa mutane su gaskata da mai zuwa bayansa, wato Yesu.”

5. Da suka ji haka, aka yi musu baftisma da sunan Ubangiji Yesu.

6. Da Bulus ya ɗora musu hannu, Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu, suka kuwa yi magana da waɗansu harsuna, suna annabci.

7. Su wajen sha biyu ne duka duka.

8. Sai ya shiga majami'a yana wa'azi gabagaɗi, ya kuma yi wata uku yana muhawwara da su, yana kuma rinjayarsu a kan al'amarin Mulkin Allah.

9. Amma da waɗansu suka taurare, suka ƙi ba da gaskiya, suna kushen wannan hanya gaban jama'a, sai ya rabu da su, ya keɓe masu bi, yana ta muhawwara da su a kowace rana makarantar Tiranas.

10. Shekara biyu ana wannan, har dukan mazaunan ƙasar Asiya suka ji Maganar Ubangiji, Yahudawa da al'ummai duka.

11. Ta hannun Bulus kuma Allah ya yi waɗansu mu'ujizai da ba a saba gani ba,

Karanta cikakken babi A.m. 19