Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 18:20-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sai suka roƙe shi ya ƙara jimawa a wurinsu, amma bai yarda ba.

21. Sai dai ya yi bankwana da su, ya ce, “Zan dawo wurinku in Allah ya so.” Sa'an nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.

22. Da ya sauka a Kaisariya, sai ya je Urushalima, ya gaisa da Ikkilisiya, sa'an nan ya tafi Antakiya.

23. Bayan da ya ɗan jima a nan, ya tashi ya zazzaga ƙasar Galatiya da ta Firijiya, yana bin gari gari, yana ƙarfafa dukan masu bi.

24. To, wani Bayahude mai suna Afolos ya zo Afisa. Shi kuwa asalinsa mutumin Iskandariya ne, masani ne kuwa, ya san Littattafai ƙwarai da gaske.

25. An karantar da shi tafarkin Ubangiji, da yake kuma muhimmanci ne ƙwarai, yakan yi ta magana kan al'amuran Yesu, yana kuma koyar da su sosai, amma fa baftismar Yahaya kaɗai ya sani.

26. Sai ya fara wa'azi gabagaɗi a majami'a, amma da Bilkisu da Akila suka ji maganarsa, suka ja shi a jika, suka ƙara bayyana masa tafarkin Allah sosai da sosai.

27. Da ya so hayewa zuwa ƙasar Akaya, 'yan'uwa suka taimake shi, suka rubuta wa masu bi wasiƙa su karɓe shi hannu biyu biyu. Da kuwa ya isa, ya yi matuƙar taimako ga waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin alherin Ubangiji,

28. don yā kayar da Yahudawa ƙwarai a gaban jama'a, yana tabbatar musu ta wurin Littattafai cewa Almasihu dai Yesu ne.

Karanta cikakken babi A.m. 18