Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 17:27-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. wato nufinsa shi ne su neme shi, ko watakila sā laluba su same shi, alhali kuwa ba ya nesa da kowane ɗayanmu.

28. Domin‘Ta gare shi ne muke rayuwa, muke motsi, muka kuma kasance,’kamar yadda waɗansu mawaƙanku ma suka ce,‘Hakika, mu ma zuriya tasa ce.’

29. To, da yake mu zuriyar Allah ne, ai, bai kamata mu tsammaci Allah na kama da wata surar zinariya, ko ta azurfa, ko ta dutse ba, wadda mutum ya ƙago ta dabararsa.

30. Dā kam, Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu yana umartar dukkan mutane a ko'ina su tuba,

31. tun da yake ya tsai da ranar da zai yi wa duniya shari'a, shari'a adalci, ta wurin mutumin nan da ya sa, wannan kuwa ya tabbatar wa dukan mutane, da ya tashe shi daga matattu.”

32. Da dai suka ji maganar tashin matattu, sai waɗansu suka yi ba'a, amma waɗansu suka ce, “Game da wannan magana kam, mā sāke jin abin da za ka faɗa.”

33. Sai Bulus ya fita daga cikinsu.

34. Amma waɗansu mutane suka koma wajensa suka ba da gaskiya, a cikinsu har da Diyonisiyas, ɗan majalisar Tudun Arasa, da wata mace mai suna Damarisa, da waɗansu dai haka.

Karanta cikakken babi A.m. 17