Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 17:21-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Alhali kuwa duk Atinawa da baƙinsu ba abin da suke yi, sai kashe zarafinsu wajen jin baƙon abu, ko kuma ɗorar da shi.

22. Sai Bulus ya miƙe a tsakiyar Tudun Arasa, ya ce, “Ya ku mutanen Atina, na dai lura, ku masoyan ibada ne ƙwarai, ta kowane fanni.

23. Don sa'ad da nake zagawa, na duba abubuwan da kuke yi wa ibada, har ma na tarar da wani bagadin hadaya da wannan rubutu a sama da shi cewa, ‘Saboda Allahn da ba a sani ba.’ To, shi wanda kuke yi wa sujada ba a tare da kun san shi ba, shi nake sanar muku.

24. Allahn da ya halicci duniya da dukkan abin da yake cikinta, shi da yake Ubangijin sama da ƙasa, ba ya zama a haikalin ginin mutum.

25. Haka kuma ba ya neman wani taimako gun mutum, sai ka ce wani abu yake bukata, tun da yake shi kansa ne yake ba dukkan mutane rai, da numfashi, da dukkan abubuwa.

26. Shi ne kuma ya halicci dukkan al'umma daga tsatso ɗaya, domin su zauna a dukan sararin duniya, ya kuma ƙayyade zamanansu da iyakokin ƙasashensu,

27. wato nufinsa shi ne su neme shi, ko watakila sā laluba su same shi, alhali kuwa ba ya nesa da kowane ɗayanmu.

28. Domin‘Ta gare shi ne muke rayuwa, muke motsi, muka kuma kasance,’kamar yadda waɗansu mawaƙanku ma suka ce,‘Hakika, mu ma zuriya tasa ce.’

29. To, da yake mu zuriyar Allah ne, ai, bai kamata mu tsammaci Allah na kama da wata surar zinariya, ko ta azurfa, ko ta dutse ba, wadda mutum ya ƙago ta dabararsa.

30. Dā kam, Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu yana umartar dukkan mutane a ko'ina su tuba,

31. tun da yake ya tsai da ranar da zai yi wa duniya shari'a, shari'a adalci, ta wurin mutumin nan da ya sa, wannan kuwa ya tabbatar wa dukan mutane, da ya tashe shi daga matattu.”

32. Da dai suka ji maganar tashin matattu, sai waɗansu suka yi ba'a, amma waɗansu suka ce, “Game da wannan magana kam, mā sāke jin abin da za ka faɗa.”

33. Sai Bulus ya fita daga cikinsu.

Karanta cikakken babi A.m. 17