Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 16:36-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Yari kuwa ya shaida wa Bulus maganar, ya ce, “Alƙalai sun aiko a sake ku, saboda haka yanzu sai ku fito, ku tafi lafiya.”

37. Amma Bulus ya ce musu, “Ai, a fili suka daddoke mu, ba ko bin ba'asi, mu ma da muke Romawa bisa ga 'yangaranci, suka jefa mu a kurkuku, yanzu kuma sā fitar da mu a ɓoye? Sai dai su zo da kansu su fito da mu.”

38. Sai dogarai suka shaida wa alƙalan wannan magana. Su kuwa da suka ji Bulus da Sila Romawa ne suka tsorata.

39. Sa'an nan suka zo suka tubar musu, bayan kuma sun fito da su, suka roƙe su su bar garin.

40. To, da suka fita daga kurkukun, suka tafi wurin Lidiya. Bayan sun ga 'yan'uwa, suka kuma ƙarfafa musu zuciya, suka tashi.

Karanta cikakken babi A.m. 16