Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 15:8-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Allah kuwa, masanin zuciyar kowa, ya yi musu shaida da ya ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu.

9. Bai kuma nuna wani bambanci tsakaninmu da su ba, tun da yake ya tsarkake zukatansu saboda bangaskiyarsu.

10. Saboda haka, don me kuke gwada Allah, ta ɗora wa almajiran nan kayan da mu, duk da kakanninmu, muka kasa ɗauka?

11. Amma mun gaskata, cewa, albarkacin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”

12. Sai duk taron mutane suka yi tsit, suka saurari Barnaba da Bulus, sa'ad da suke ba da labarin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi, da Allah ya yi ga al'ummai ta wurinsu.

13. Bayan sun gama jawabi, Yakubu ya amsa ya ce, “Ya ku 'yan'uwa, ku saurare ni.

14. Bitrus ya ba da labari yadda Allah ya fara kula da al'ummai, domin ya keɓe wata jama'a daga cikinsu ta zama tasa.

15. Wannan kuwa daidai yake da maganar annabawa, yadda yake a rubuce cewa,

16. ‘Bayan haka kuma zan komo,In sāke gina gidan Dawuda da ya rushe,In sāke ta da kangonsa,In tsai da shi,

17. Domin sauran mutane su nemi Ubangiji,Wato al'umman da suke nawa.’

18. Haka Ubangiji ya ce, shi da ya bayyana waɗannan abubuwa tun zamanin dā.

19. Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa al'ummai waɗanda suke juyowa ga Allah,

20. sai dai mu rubuta musu wasiƙa, su guji abubuwan ƙazanta na game da gumaka, da fasikanci, da cin abin da aka maƙure, da kuma cin nama tare da jini.

21. Domin tun zamanin dā, a kowane gari akwai masu yin wa'azi da littattafan Musa, ana kuma karanta su a majami'u kowace Asabar.”

Karanta cikakken babi A.m. 15