Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 15:20-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. sai dai mu rubuta musu wasiƙa, su guji abubuwan ƙazanta na game da gumaka, da fasikanci, da cin abin da aka maƙure, da kuma cin nama tare da jini.

21. Domin tun zamanin dā, a kowane gari akwai masu yin wa'azi da littattafan Musa, ana kuma karanta su a majami'u kowace Asabar.”

22. Sai manzanni da dattawan Ikkilisiya, tare da dukan 'yan Ikkilisiya, suka ga ya kyautu su zaɓi waɗansu daga cikinsu, su aike su Antakiya tare da Bulus da Barnaba. Sai suka aiki Yahuza, wanda ake kira Barsaba, da kuma Sila, shugabanni ne cikin 'yan'uwa,

23. da wannan takarda cewa, “Daga 'yan'uwanku, manzanni da dattawan Ikkilisiya, zuwa ga 'yan'uwanmu na al'ummai a Antakiya da ƙasar Suriya da ta Kilikiya. Gaisuwa mai yawa.

24. Tun da muka sami labari, cewa waɗansu daga cikinmu sun ta da hankalinku da maganganu, suna ruɗa ku, ko da yake ba mu umarce su da haka ba,

25. sai muka ga ya kyautu, da yake bakinmu ya zo ɗaya, mu aiko muku waɗansu zaɓaɓɓun mutane, tare da ƙaunatattunmu Barnaba da Bulus,

26. waɗanda suka sayar da ransu saboda sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu.

27. Don haka, ga shi, mun aiko muku Yahuza da Sila, su ma za su gaya muku waɗannan abubuwa da bakinsu.

28. Domin Ruhu Mai Tsarki ya ga ya kyautu, mu ma mun gani, kada a ɗora muku wani nauyi fiye da na waɗannan abubuwa da suke wajibi, wato

29. ku guji abin da aka yanka wa gunki, da cin nama tare da jini, da cin abin da aka maƙure, da kuma fasikanci. In kun tsare kanku daga waɗannan, za ku zauna lafiya. Wassalam.”

Karanta cikakken babi A.m. 15