Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 14:6-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. suka sami labari, suka gudu zuwa biranen Likoniya wato Listira da Darba, da kuma kewayensu.

7. Nan suka yi ta yin bisharar.

8. To, a Listira akwai wani mutum a zaune, wanda ƙafafunsa ba su da ƙarfi, gurgu ne tun da aka haife shi, bai ma taɓa tafiya ba.

9. Yana sauraron wa'azin Bulus, sai Bulus ya zuba masa ido, da ya ga bangaskiyarsa ta isa a warkar da shi,

10. ya ɗaga murya ya ce, “Tashi, ka tsaya cir.” Sai wuf ya zabura, har ya yi tafiya.

11. Da taron suka ga abin da Bulus ya yi, suka ɗaga murya gaba ɗaya suna cewa da Likoniyanci, “Lalle, alloli sun sauko mana da siffar mutane!”

12. Sai suka ce Barnaba shi ne Zafsa, Bulus kuwa don shi ne shugaban magana, wai shi ne Hamisa.

Karanta cikakken babi A.m. 14