Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 14:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, a Ikoniya suka shiga majami'ar Yahudawa tare, suka yi wa'azi, har mutane masu yawa, Yahudawa da al'ummai, suka ba da gaskiya.

2. Amma Yahudawa da suka ƙi bi, suka zuga al'ummai, suka ɓata tsakaninsu da 'yan'uwa.

3. Sai Bulus da Barnaba suka daɗe a nan ƙwarai, suna wa'azi gabagaɗi bisa ga ikon Ubangiji, shi da ya shaida maganar alherinsa ta yarjin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi ta hannunsu.

4. Amma mutanen birni suka rarrabu, waɗansu suka koma bayan Yahudawa, waɗansu kuma bayan manzannin.

5. Sa'ad da al'ummai da Yahudawa tare da shugabanninsu suka tasar wa manzannin, su wulakanta su, su jejjefe su da duwatsu,

6. suka sami labari, suka gudu zuwa biranen Likoniya wato Listira da Darba, da kuma kewayensu.

7. Nan suka yi ta yin bisharar.

8. To, a Listira akwai wani mutum a zaune, wanda ƙafafunsa ba su da ƙarfi, gurgu ne tun da aka haife shi, bai ma taɓa tafiya ba.

9. Yana sauraron wa'azin Bulus, sai Bulus ya zuba masa ido, da ya ga bangaskiyarsa ta isa a warkar da shi,

Karanta cikakken babi A.m. 14