Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 12:7-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. sai ga mala'ikan Ubangiji tsaye kusa da shi, wani haske kuma ya haskaka ɗakin, sa'an nan mala'ikan ya bugi Bitrus a kwiɓi, ya tashe shi, ya ce, “Maza, ka tashi.” Sai kuwa sarƙar ta zube daga hannunsa.

8. Mala'ikan ya ce masa, “Yi ɗamara, ka sa takalminka.” Sai ya yi. Sai ya ce masa, “Yafa mayafinka, ka biyo ni.”

9. Sai ya fito ya bi shi, bai san abin da mala'ikan nan ya yi hakika ne ba, cewa yake wahayi ake yi masa.

10. Da suka wuce masu tsaron farko da na biyu, suka isa ƙyauren ƙarfe na ƙofar shiga gari, ƙyauren kuwa ya buɗe musu don kansa. Sai suka fita. Sun ƙure wani titi ke nan, nan da nan sai mala'ikan ya bar shi.

11. Da Bitrus ya koma cikin hankalinsa, ya ce, “Yanzu kam na tabbata, Ubangiji ne ya aiko mala'ikansa, ya cece ni daga hannun Hirudus, da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.”

12. Da ya gane haka, ya je gidan Maryamu, uwar Yahaya wanda ake kira Markus, inda aka taru da yawa, ana addu'a.

13. Da ya ƙwanƙwasa ƙofar zauren, wata baranya mai suna Roda ta zo ji ko wane ne.

Karanta cikakken babi A.m. 12