Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 12:10-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Da suka wuce masu tsaron farko da na biyu, suka isa ƙyauren ƙarfe na ƙofar shiga gari, ƙyauren kuwa ya buɗe musu don kansa. Sai suka fita. Sun ƙure wani titi ke nan, nan da nan sai mala'ikan ya bar shi.

11. Da Bitrus ya koma cikin hankalinsa, ya ce, “Yanzu kam na tabbata, Ubangiji ne ya aiko mala'ikansa, ya cece ni daga hannun Hirudus, da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.”

12. Da ya gane haka, ya je gidan Maryamu, uwar Yahaya wanda ake kira Markus, inda aka taru da yawa, ana addu'a.

13. Da ya ƙwanƙwasa ƙofar zauren, wata baranya mai suna Roda ta zo ji ko wane ne.

14. Da ta shaida muryar Bitrus, ba ta buɗe ƙofar ba don murna, sai ta koma ciki a guje, ta ce Bitrus na tsaye a ƙofar zaure.

15. Sai suka ce mata, “Ke dai akwai ruɗaɗɗiya.” Ita kuwa ta nace a kan shi ne. Su kuwa suka ce, “To, mala'ikansa ne!”

16. Bitrus dai ya yi ƙwanƙwasawa, da suka buɗe suka gan shi, suka yi ta al'ajabi.

Karanta cikakken babi A.m. 12