Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 5:22-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, Ubangiji ke nan kuke yi wa.

23. Don miji shi ne shugaban matarsa, kamar yadda Almasihu yake shugaban Ikkilisiya, wato, jikinsa, shi kansa kuma shi ne Mai Ceton jikin.

24. Kamar yadda Ikkilisiya take bin Almasihu, haka kuma mata su bi mazansu ta kowane hali.

25. Ku maza, ku ƙaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya ƙaunaci ikkilisiya, har ya ba da kansa dominta,

26. domin ya miƙa ta ga Allah, tsarkakakkiya bayan da ya wanke ta da ruwa ta wurin Kalma,

27. domin shi kansa yă ba kansa Ikkilisiya da ɗaukakarta, ba tare da tabo ko tamoji ba, ko wani irin abu haka, tă dai zamo tsattsarka marar aibu.

28. Ta haka ya wajaba maza su ƙaunaci matansu, jikinsu ke nan suke yi wa. Ai, wanda ya ƙaunaci matarsa, ya ƙaunaci kansa ke nan.

29. Domin ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai ya rene shi, ya yi tattalinsa, kamar yadda Almasihu yake yi wa Ikkilisiya,

30. domin mu gaɓoɓin jikinsa ne.

31. “Saboda haka ne, mutum sai ya bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya manne wa matarsa, su biyu su zama jiki guda.”

32. Wannan asiri muhimmi ne, ni kuwa ina nufin Almasihu ne da ikkilisiya.

Karanta cikakken babi Afi 5