Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 4:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Don haka, ni ɗan sarƙa saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi zaman da ya cancanci kiran da aka yi muku,

2. da matuƙar tawali'u, da salihanci, da haƙuri, kuna jure wa juna saboda ƙauna.

3. Da ƙwazo ku kiyaye ɗayantuwar da Ruhu yake zartarwa, kuna a haɗe a cikin salama.

4. Jiki guda ne, Ruhu kuma guda, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan guda, wanda yake game da kiran nan.

5. Ubangiji guda ne, bangaskiya guda, da kuma baftisma guda.

6. Allah ɗaya ne, Ubanmu duka, wanda yake bisa duka, ta wurin duka, a cikin duka kuma.

7. Amma an ba kowannenmu alheri gwargwadon baiwar Almasihu.

8. Saboda haka, Nassi ya ce,“Sa'ad da ya hau Sama ya bi da rundunar kamammu,Ya kuma yi wa 'yan adam baye-baye.”

9. (Wato, da aka ce “ya hau” ɗin, me aka fahimta, in ba cewa dā ya sauka a can ƙasa ba?

10. Shi wanda ya sauka ɗin, shi ne kuma ya hau a can birbishin dukkan sammai, domin yă cika kome.)

11. Ya kuma yi wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu annabawa, waɗansu masu yin bishara, waɗansu makiyaya masu koyarwa,

12. domin tsarkaka su samu, su iya aikin hidimar Ikkilisiya, domin a inganta jikin Almasihu,

13. har mu duka mu riski haɗa kan nan na bangaskiya ga Ɗan Allah, da kuma saninsa, mu kai maƙamin cikakken mutum, mu kuma kai ga matsayin nan na falalar Almasihu.

14. An yi wannan kuwa don kada mu sāke zama kamar yara, waɗanda suke jujjuyawa, iskar kowace koyarwa tana ɗaukar hankalinsu, bisa ga wayon mutane da makircinsu da kissoshinsu.

15. A maimakon haka, sai mu faɗi gaskiya game da ƙauna, muna girma a cikinsa ta kowace hanya, wato Almasihu, shi da yake shugabanmu.

Karanta cikakken babi Afi 4