Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 2:14-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Domin Almasihu shi ne salamarmu, shi wanda ya mai da Yahudawa da al'ummai ɗaya, wato ya rushe katangar nan da ta raba su a kan gāba.

15. Har ya soke Shari'ar nan mai umarni da dokoki, ta wurin ba da jikinsa, domin ta gare shi yă halicci sabon mutum guda daga mutanen nan biyu, ta haka yă kawo salama,

16. yă kuma sulhunta su duka biyu ga Allah, su zama jiki ɗaya ta wurin gicciye, ta haka yă kashe gābar.

17. Ya kuwa zo ya yi muku albishirin salama, ku da kuke nesa, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa.

18. Domin ta gare shi ne dukanmu biyu muka sami isa gun Uba ta hanyar Ruhu guda.

19. Wato ashe, ku ba baƙi ba ne kuma, ko kuwa bāre, ai, ku abokan 'yanci ne na tsarkaka, iyalin Allah kuma,

Karanta cikakken babi Afi 2