Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tim 1:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. wanda ya cece mu, ya kuma kira mu da kira mai tsarki, ba don wani aikin lada da muka yi ba, sai dai domin nufinsa, da kuma alherinsa, da aka yi mana baiwa tun fil'azal, a cikin Almasihu Yesu,

10. wadda a yanzu aka bayyana ta bayyanar Mai Cetonmu Almasihu Yesu, wanda ya shafe mutuwa, ya kuma bayyana rai da rashin mutuwa, ta wurin bishara.

11. A wannan bishara an sa ni mai wa'azi, da kuma manzonta, da mai koyarwarta kuma.

12. Saboda haka, ne nake shan wuya haka. Duk da haka, ban kunyata ba, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata yana da iko ya kiyaye abin da na danƙa masa, har ya zuwa waccan rana.

13. Ka yi koyi da sahihiyar maganar da ka ji daga gare ni, da bangaskiya da ƙauna da take ga Almasihu Yesu.

14. Kyakkyawan abin nan da aka ba ka amana, ka kiyaye shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki, wanda yake zaune a zuciyarmu.

15. Ka dai sani duk waɗanda suke ƙasar Asiya sun juya mini baya, a cikinsu kuwa har da Fijalas da kuma Harmajanas.

16. Ubangiji yă yi wa iyalin Onisifaras jinƙai, don sau da yawa yake sanyaya mini zuciya, bai kuwa ji kunyar ɗaurina da aka yi ba.

17. Har ma da ya zo Roma, sai ya neme ni ido a rufe, ya kuwa same ni.

18. Ubangiji ya yi masa jinƙai a waccan rana. Ka dai sani sarai yadda ya yi ɗawainiya mai yawa a Afisa.

Karanta cikakken babi 2 Tim 1