Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tas 2:8-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. A sa'an nan ne fa sarkin tawayen zai bayyana, Ubangiji Yesu kuwa zai hallaka shi da hucin bakinsa, ya kuma shafe shi da bayyanarsa a ranar komowarsa.

9. Mai tawayen nan kuwa, zai zo ne bisa ga ikon Shaiɗan, yana aikata abubuwan al'ajabi, da alamu, da aikin dabo na ƙarya iri iri,

10. yana kuma yaudarar waɗanda suke a hanyar hallaka, muguwar yaudara, domin sun ƙi ƙaunar gaskiya har yadda za su sami ceto.

11. Saboda haka, Allah zai auko musu da wata babbar ɓatan basira don su gaskata ƙarya,

12. don duk a hukunta waɗanda suka ƙi gaskata gaskiya, suke kuma jin daɗin mugunta.

13. Ya ku 'yan'uwa, ƙaunatattun Ubangiji, lalle ne kullum mu gode wa Allah saboda ku, domin Allah ya zaɓe ku, don ku fara samun ceto ta wurin tsarkakewar Ruhu, da kuma amincewarku da gasikya.

14. Domin wannan maƙasudi ya kira ku, ta wurin bishararmu, domin ku sami ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

15. Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku dage, ku kuma riƙi ka'idodin da muka koya muku kankan, ko da baka ko ta wurin wasiƙa.

16. To, Ubangijinmu Yesu Almasihu kansa, da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu, ya kuma ba mu madawwamiyar ta'aziyya da kyakkyawan bege ta wurin alherinsa,

Karanta cikakken babi 2 Tas 2