Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tas 1:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Bulus, da Sila, da Timoti, zuwa ga Ikkilisiyar Tasalonikawa, wadda take ta Allah ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu.

2. Alheri da salama na Allah Uba, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

3. Lalle ne a kullum mu gode wa Allah saboda ku, 'yan'uwa, haka kuwa ya kyautu, da yake bangaskiyarku haɓaka take yi ƙwarai da gaske, har ma ƙaunar kowane ɗayanku ga juna ƙaruwa take yi.

4. Saboda haka, mu kanmu ma taƙama muke yi da ku a cikin ikilisiyoyin Allah, saboda jimirinku, da bangaskiyarku a cikin yawan tsananin da kuke sha, da ƙuncin da kuke a ciki.

5. Wannan kuwa ita ce tabbatar hukunci mai adalci na Allah, domin a lasafta ku a cikin waɗanda suka cancanci zama a Mulkin Allah, wanda kuke shan wuya dominsa,

6. domin kuwa Allah ya ga adalci ne, yă yi sakamokon ƙunci ga waɗanda suke ƙuntata muku,

7. yă kuma ba ku hutu har da mu ma, ku da ake ƙuntata wa ɗin, a ranar bayyanar Ubangiji Yesu daga Sama tare da manyan mala'ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa,

8. yana ta sāka wa waɗanda suke ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suka ƙi bin bisharar Ubangijinmu Yesu.

9. Za su sha hukuncin madawwamiyar hallaka, suna a ware da zatin Ubangiji, da kuma, maɗaukakin ikonsa,

Karanta cikakken babi 2 Tas 1