Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 8:13-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ba nufi nake yi a sawwaƙe wa waɗansu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba.

14. Amma don a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu, don wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita al'amari.

15. Yadda yake a rubuce cewa, “Wanda ya tara mai yawa, bai fi bukatarsa ba, wanda ya tara kaɗan kuwa, ba abin da ya gaza masa.”

16. Godiya tā tabbata ga Allah wanda ya sa tsananin kula da ku a zuciyar Titus, kamar yadda nake yi.

17. Ba kuwa na'am da roƙonmu kaɗai ya yi ba, har ma saboda tsananin himma tasa yana zuwa wurinku da ra'in kansa.

18. Ga shi, mun aiko ɗan'uwan nan tare da shi, wanda ya yi suna wajen yin bishara a dukan ikilisiyoyi,

19. ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikilisiyoyi sun zaɓe shi ya riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu.

20. Wato, muna gudun kada kowa yă zarge mu a kan kyautan nan da ake yi hannu sake, wadda muke kasaftawa.

21. Niyyarmu ce mu yi abubuwan da suke daidai, ba wai a gaban Ubangiji kaɗai ba, har ma a gaban mutane.

22. Muna kuma aiko da ɗan'uwanmu tare da su, wanda sau da yawa muka tabbatar da himma tasa ta hanya iri iri, yanzu kuma ya fi koyaushe himma, domin amincewa da ku da yake yi ƙwarai da gaske.

23. Titus kuwa, ai, abokin tarayyata ne, abokin aikina kuma game da al'amuranku. 'Yan'uwan nan namu kuwa, ai, manzanni ne na ikilisiyoyi, masu ɗaukaka Almasihu.

24. Saboda haka sai ku tabbatar wa waɗannan mutane a gaban ikilisiyoyi irin ƙaunarku, da kuma cewa taƙama da ku da muke yi gaskiya ce.

Karanta cikakken babi 2 Kor 8