Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 7:6-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Amma Allah, shi da yake ƙarfafa wa ƙasƙantattu zuciya, sai ya ƙarfafa mana zuciya da zuwan Titus,

7. ba kuwa da zuwan Titus kawai ba, har ma a game da ƙarfafa zuciyar nan da ya samu a wurinku, a yayin da ya gaya mana yadda kuke begena, kuna nadama, kuna kuma himmantuwa ga goyan bayana, har ma na ƙara farin ciki ƙwarai.

8. Ko da na ɓata muku rai a game da wasiƙar da dā na rubuto muku, ba na baƙin ciki da haka, ko da yake dā kam na yi baƙin ciki, don na lura wasiƙar nan ta ɓata muku rai, ko da yake dai zuwa ɗan lokaci kaɗan ne.

9. Amma a yanzu kam, ina farin ciki, ba don kun yi baƙin ciki ba, sai dai don baƙin cikinmu ya sa ku tuba, don kun yi baƙin ciki irin wanda Allah yake so. Saboda haka, ba ku yi hasarar kome a sanadinmu ba.

10. Don baƙin ciki irin wanda Allah yake sawa, shi ne yake biyarwa zuwa ga tuba, da kuma samun ceto, ba ya kuma sa “da na sani”. Amma baƙin ciki a kan al'amarin duniya, yakan jawo mutuwa.

11. Ku dubi fa irin himmar da baƙin cikin nan, da Allah yake so ya sa a zukatanku, da irin ɗokin da kuka yi na gyara al'amuranku, da irin haushin da kuka ji, da irin tsoron da kuka ji, da irin begen da kuka yi, da irin himmar da kuka yi, da kuma irin niyyarku ta horo. A game da wannan sha'ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi.

Karanta cikakken babi 2 Kor 7