Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 7:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya ku ƙaunatattu, tun da aka yi mana waɗannan alkawarai, sai mu tsarkake kanmu daga kowace irin ƙazanta ta jiki ko ta zuci, da bangirma ga Allah mu kamalta a cikin tsarki.

2. Ku saki zuciya da mu, ai, ba mu cuci kowa ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu zambaci kowa ba.

3. Ba don in sa muku laifi na faɗi haka ba, don dā ma na gaya muku, abin ƙauna kuke a gare mu ƙwarai, ko a mace ko a raye, ba mu rabuwa.

4. Na amince da ku ƙwarai, ina kuma taƙama da ku gaya. Zuciyata ta ƙarfafa ƙwarai. Duk da wahalce-wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske.

5. Ko a lokacin da muka zo ƙasar Makidoniya ma, ba mu sami shaƙatawa ba, ana ta wahalshe mu ta kowace hanya, a waje ga husuma, a zukatanmu kuma ga fargaba.

Karanta cikakken babi 2 Kor 7